A cikin kowane bangare na rayuwa akwai wanda suke fice akan saura, a bangaren cryptocurrency ma ba’abarsu a baya ba. A wannan post din zamu ga mutane 8 da sukayi fice ta bangaren arziki a duniyar crypto.

1: Satoshi Nakamoto – $55.34 billion

Shahararren shehin malamin Computer wato Satoshi Nakamoto kuma wanda ya kirkiri fasahar Blockchain yana rike da matsayi na daya yayin da ake tsegemun cewa yana rike da fiye da bitcoin miliyan daya wanda kimaninsu ya kai dala  Biliyan ($55.00B).

Yana da matukar wahala a tantance ainihin adadin Bitcoins da Satoshi yake rike da shi, A zahiri, Satoshi bai taɓa taɓa bitcoin ɗin shi ba, da wannan ne masu sa’ido suke ta’alikin duk wani addreshi da ba’a taba komai a cikinsa ba da cewar na Satoshi ne.

Rashin taba ko da ƙaramin adadin Bitcoin da ke karkashin mallakin Satoshi na daga cikin abinda ya baiwa Bitcoin farashinsa na yau ba tare da ya rushe` ba.

Rashin sanin wane ne Satoshi, hade da rashin taba komai da ke cikin addreshin da ke dauke da Bitcoin dinsa na daga cikin alamu da ke nuna cewa tabbas Bitcoin kudi ne na jama’a, don jama’a kuma saboda jama’a.

Mahukunta na daf da tallafawa Bankuna a karo na biyu (kafin rugujewar kasuwar duniya).

― Satoshi Nakamoto

2: Brian Armstrong – $6.5B

Wataƙila kun ji sunan Brian Armstrong dangane da sanannen dandamalin bitcoin wato Coinbase. Wannan saboda Brian shine Shugaba kuma wanda ya kafa 1dandamalin Coinbase. Ya fara Coinbase tare da abokin aikinsa Fred Ersam a cikin 2012 bayan ya bar aikinsa a AirBnB.

Brian ya mallaki kaso 20% na coinbase, a cewar Brian, “Ina so a sami budaddiyar tsarin kudi a duniyar da muke ciki, wanda ke cike da kirkira da ‘yanci”

Brian Armstrong mutum ne da aka sani wajen kyauta da sadaukar da dukiyarsa wajen tallafawa marasa galihu. Brian na daya daga cikin yan crypto da yayi fice a wannan harka ta tallafawa gajiyayyu.

  

3: Roger Ver – $5.5B

Shin ko kun taba jin sunan “Al-masihu ko Yesun Bitcoin” Idan baka taba ji ba to wannan shi ne inkiyar Rоgеr Viya wannan inkiyar ya samo asali ne saboda busharar da Roger ya yayata na zuwan Bitcoin da gagarumin iliminsa har ake alakanta shi da busharar da almasihu ya kawo na hasken addini da tsarkakewa.

Roger na daga cikin farkon wanda suka shiga bitcoin, kuma ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan sa. An san shi da yada bisharar bitcoin mai kyau, (haka Yesu), da ba da bitcoin kyauta.

Akwai yiwuwar cewa, Roger Viya ya yi dalilin shigar mutane zuwa bitcoin sama da kowa a fadin duniya Kodayake wasu suna ganin Andreyas Antonopolous ya doke shi wajen Busharar Bitcoin da Blockchain.

Yayin da rahotanni suka bambanta akan ainihin adadin Bitcoin Roger Ver yana da, an kiyasta ya kasance sama da dubu dari (100k).

A daya 1 ga watan Agustar 2017, Bitcoin ta fashe zuwa gida biyu inda aka samo Bitcoin Cash, Roja ya saida adadi mai yawa na Bitcoin dinsa zuwa Bitcoin Cash.  Roja ya kasance mutum ne mai jajircewa da son ganin karbuwar fasahar Blockchain.

Roger ya dage kan yin amfani da fasahar Blockchain wajen kawar da gurbatattun kudaden ajiyar gwamnati.

4: Sam Bankman-Fried – $4.5B

A karancin shekaru da baifi 28 da haihuwa ba, matashin dan kasuwa Sam Bankman yana kula da sama da dala $2.5 billion a karkashin kamfanin Alameda Research, kamfanin crypto da ya kirkiro a shekarar 2017.

Tshohon dalibin MIT, kuma tsohon dan kasuwan ETF na Wall Street, shi ya kirkiro dandamalin FTX a shekarar 2019.

Kaso mafi yawa na kudin Sam Bankman ya samo asali daga ribar da ya samu daga ribar coin dinsa na FTX da FTT.

5: Chris Larsen – $2.9 B

Сhrіѕ Lаrѕеn Ba’amurke ne da yayi fice wajen tsintar sababbin kamfanunuka a silicon Valley, wanda daga baya suke samun gagarumun nasara. Daga cikin kamfani da ya samo shi ne Е-Lоаn a shekarar 1997, dandamali ne na bada rance kuma ya ci gaba da aiki har 2012.

A 2012 Chris da abokinsa Jed Macaleb suka kirkiro Ripple don amfani dashi wajen tura kudi zuwa ketare ta hanyar amfani da kafar blockchain. A janairun 2018 kimar Chris ya kai 17B, amma bayan rushewar kasuwar crypto, Hukumar tantancezuba hannun jari na America suka kakaba Larsen a kotu don tuhumarsa wajen saida hannun jari ba tare da cikakken izini ba.

Larsen yace dangane da wannan tuhuma, “Lallai SEC sun yi kuskure akan hujjojinsu da gudanar da doka”.

6: Champeng Zhao (CZ) –  $1.9B

Champeng Zhao wanda aka fi sani da CZ – Tsohon masanin computer, ya saida gidansa da ke garin Shanghai a 2014 inda ya zuba dukkan kudin a cikin Bitcoin. Jimawa kadan Bitcoin ya rushe daga $$ zuwa $ amma wannan bai sa CZ ja da baya ba.

CZ dai yaron Farfesa ne da aka kora a China, yayi aikin gasa gurasa a Macdonals da kuma aikin bunburutu don kula da daiwainiyarsa.

Ya yi aiki na wani lokaci a karkashin OKEX kafin bude nashi kasuwar mai suna Binance a kakar 2017, a kasa da wata shida Binance ta samu karbuwa a matsayin babban kasuwar crypto a duniya.

Bayan wannan gagarumin nasara, Binance ta maida karfi wajen zuba hannun jari akan sababbin company da suke da alaka da zabarin Bitcoin da kirkiro katin cire kudin Bitcoin wanda zai baka damar cire kudi a koina a Europe.

CZ na daya daga cikin mutane da suka taki sa’a a crypto.

7: Tagwaye Kameron da Tyla Winklevoss – $1.6

Tagwayen Winklevoss sun shahara saboda karar da suka shigar na Facebook akan satar fasaharsu da yayi na kirkirar faecbook, inda kotu tasa aka ba su kyautar kusan dala miliyan 65. Nan take tagwayen suka dauki wannan kudin suka sayi bitcoin da shi. Sun sayi kusan kashi 1% na adadin kuɗin bitcoin, wanda ya kai 70,000.

Tun daga wannan lokacin, sun saka hannun jari a cikin farawa masu alaƙa da bitcoin da yawa, da kuma fara nasu dandamalin hada-hadar crypto mai suna; Gemini.

Yanzu, Kameron da Tyla suna ciyar da lokacinsu don gina dandamalin nasu da kuma hanzarta karɓar bitcoin da fasahar cryptocurrency masu alaƙa. Nasarar da suka yi na baya-bayan nan a cikin sararin crypto shine haɗin gwiwa tsakanin Gemini da Wealth Simple Canada.

A yanxu haka dandamalin Gemini yana hada-hadar sama da miliyan 200 a yini.

8: Barry Silbert – $1.5 B

Ɗaya daga cikin ƙananan sanannun suna, amma ayyukansa sun taimaka matuka a duniyar crypto. Wanan ba kowa bane face Barry Silbert.

Barry na daga cikin mutanen farko da suka zuba hannun jari a kamfanoni masu girma kuma na farko wajen haɓaka harkan crypto kamar Coinbase, Ripple, da BitPay.

A cikin 2013 Barry ya kafa kamfanin hannun jarin Bitcoin na GrayScale. Grayscale yana siyan bitcoin da sauri fiye da yadda ake hakowa. Idan saurin tarin su ya ci gaba, za su mallaki har zuwa 3% na jimlar adadin bitcoin nan da Janairu 2021. Idan saurin jarin su ya ci gaba har tsawon shekaru da yawa, to a ƙarshe za su mallaki bitcoin fiye da Satoshi Nakamoto.

Yana da kyau a faɗi cewa yayin da Barry da kansa yana da ƙima na Bitcoin, ya shiga jerin sunayen ne saboda Grayscale.

9: Jed  Mcaleb – $1.4B

Jed na daga cikin fitattu da suka yi suna a farkon fitowar Bitcoin. Ya taimakawa Chris Larsen wajen kirkiro Kamfanin Ripple a 2012 kafin daga bisani, sabani ya sa Jed barin Ripple inda ya kirkiri nashi kamfani mai suna Stellar Lumens (XLM) wanda shi ma yana aiki ne wajen saukaka tura kudi zuwa kasashen waje ta hanyar amfani da fasahar Blockchain.

Kaso mai yawa na kudin Jed ya samo asali ne daga hannun jari da ya zuba a lokacin da yake kamfanin Ripple wanda kimaninsu ya kai $1.4B.

Leave a Comment