

Bayan shafe sama da watanni al-ummar crypto daban daban na Arewa na ta kokarin ganin alfanun crypto ya samu karbuwa da kuma gusar da kazantar shitcoins da tsare-tsaren pyramid schemes da investment platforms, Makarantar Bitkova tayi namijin kokari wajen kaddamar da taro na musamman don wayar da kan al-umma da bijiro musu da damammaki da ke da akwai a duniyar cryptocurrency.
Cikin karfin Allah taro ya sami halartar sama da mutane 150 daga manazarta, sabbin shiga har da masu fada aji a duniyar crypto a Nigeria kamar su Malam Bello Kano, Malam Adedeji Owonebi, Malam Sunusi Danjuma Ali da ma masana a wannan harka.
Mun sami bakwancin manyan projects kamar su OKX, Minaland da NEAR Protocol.
Muna fatan a sake yin taro irin wannan a karo a na gaba a cikin Arewa don a Kara wayar da kan al-umma akan tarin amfani da ke duniyar cryptocurrrency.
- This event has passed.
-
Cost
Free -
Start Time
December 18 - 11:00 am -
End Time
December 18 - 2:00 pm -
Phone
08036107361 -
Organizer
Makarantar Bitkova